WATA SABUWA: Ganduje da mataimakin sa Hafiz Bello sun Cukuikuye

0

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya nuna rashin jin dadin sa ga kalaman da mataimakin sa yayi a kafafen yada labarai cewa ba zai yi takara da shi ko ya ne me shi da haka a 2019.

Ganduje ya ce abin ya sashi cikin dimuwa ganin cewa mataimakin sa ne ya ke fadin irin wadannan maganganu.

Hafiz Bello ya zargi gwamnatin Ganduje da nuna masa wariya a ayyukan gwamnati da siyasar Kano.

Ya koka da yadda a kayi amfani da karfin gwamnati wajen korar wani shugaban jam’iyyar APC na mazabar sa, Mandawari.

Gwamna Ganduje ya bada umurnin maida wanda a ka kora sannan ya gargadi masu yin amfani da kujerun su wajen aikata wasu abubuwa da bashi da masaniya akai da su raba kan su da haka.

Ya ce daga yanzu duk wani abu da za a gudanar na jam’iyyar a tabbata an sanar da shi.

Kwamishinan Al’adu Muhammed Garba ne ya sanar da haka a madadin gwamna Ganduje.

Share.

game da Author