Wasu likitoci a jami’ar ‘Johns Hopkins Bloomberg School of Public Health’ dake Maryland kasar Amurka sun gano cewa cin danyan tumatir da kayan lambu na inganta huhun dan Adam.
Likitocin sun bayyana cewa cin danyan tumatir na kare mutum daga kamuwa da cutukan dake kama zuciya da huhu musamman ga masu zukar taba sigari ko kuma wadanda suka daina shan sigari.
Likitocin sun bayana cewa kimiya ta bayyana cewa huhun mutum takan fara kamuwa da cututtuka irin haka ne daga shekaru 30 ko da baya amfani da sigari.
Sakamakon hakan ne ya sa suka gudanar da bincike don gano hanyoyin guje wa irin haka.
An gudanar da bincike ta hanyar ciyar da wasu mutane 650 kasashen Britaniya, Norway da Jamus wadanda suka tabbatar da cewa suna shan taba sigari har na shekara 10.”
Bayan wadannan tsawon shekaru ne suka gano cewa matsalolin kamuwa da irnin wadannan cututtukan zuciya da huhu dake kama mutum daga shekaru 30 ya ragu sannan kariyar da huhun ta samu sanadiyyar hakan zai kai na tsawon shekaru 10.
Saboda haka ne shugaban likitocin Garcia-Larsen take kira ga mutane da su dunga cin kayan lambu musamman danyen tumatir saboda inganta huhun da yake yi a jikin mutum.