Tsohon ministan tsaro Theophilus Danjuma ya ce daya daga cikin dalilan da ya sa ya gina sabuwar asbiti shine don samar wa mata masu ciki a garin Takum kula da samar da raguwa a mace-macen mata masu ciki da ake fama dashi saboda rashin kula da basu samu.
Ya rada wa asibitin sunar Mahaifiyar sa wato ‘Asibitin Rifikatu Danjuma.’
Danjuma ya kara da cewa bincike ya nuna mata 800 ne ke rasa rayukan su a dalilin matsalolin haihuwa da sukan fuskan ta sannan kasashe masu tasowa ne suka fi fama da wannan matsaloli.
Bayan haka gwamnan jihar Darius Ishaku ya yaba wa Danjuma game da ginin asibitin da kuma samamr musu da motocin daukar marasa lafiya da gina gidajen likitoci da masu aiki a asibitin.
Daga karshe shugaban kungiyar ‘Development Africa’ Joshua Kempeneer ya ce kungiyar za ta ci gaba da kula da asibitin har na tsawon shekaru 5.
Discussion about this post