Kungiyar likitocin kasar nan NMA da kungiyar likitocin hakora na Najeriya MDCN sun gargadi majalisar dattijai kan yi musu ‘shiga sharo ba shanu’ game da horar da likitoci a kasar nan.
Kungiyoyin su ce dokar da ta kafa su ta basu damar horar wa da tantance likitoci da bai kamata majalisar ta tsoma bakin ta ba.
Idan ba a manta ba jiya Talata kwamitin kiwon lafiya na majalisar dattijai ta yin bincike kan aiyukkan shugaban kungiyar MDCN, Tajudeen Sanusi.
Ana zargin Sanusi ne da laifin kada dalibai da suka karanta aikin likita daga makarantun kasashen waje da babu gaira babu dalili a jarabawar kwarewa a aikin likitanci da suka rubuta a asibitin koyarwa na jami’ar Ilori UITH a makon da ya gabata.
Da yake nuna fushin sa akan abin da majalisar ke nema tayi wa shugaban kungiyar, mataimakin shugaban kungiyar Kingsley Enweremadu ya ce wasu iyaye ne suka tsokata wa majalisar cewa wai an kada ‘ya’yan su da gangar shine ya sa su kuma suka harzuka su sa kungiyar a gaba.
Ya ce irin haka ya faru ga dalibai ‘yan asalin kasara Ghana, a can Ghana amma baka ji komai ba sai Najeriya.
“Idan har dai majalisa ta fara tsoma mana baki cikin aiyukkan mu toh nan gaba abin sai an dinga hadawa da zuwa kotu kenan.”
Kingsley yace duk da cewa sun yi bakin ciki game da fadin da daliban bazai yiwu a bar su kokuwa a sa musu sun ci ba ganin inda za su dosa ya shafi rayuwar mutane ne.
Kungiyar ta roki majalisar da su dakatar da wannan bincike domin ba zai hafi da mai ido ba.