Trump ya kira ‘yan Najeriya ‘mutanen daji’

0

Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya mutanen daji ne da ke zaune a cikin bukkoki.

Jaridar New York Times ta jiya Asabar, ta buga wani labari wanda ta bayyana cewa Trump ya yi wannan kalami ne a wani taro a baya dangane da kakaba takunkumin shiga Amurka wanda Trump ya yi wa wasu kasashe, bayan hawan sa mulki.

Jaridar ta ruwaito cewa Trump ya kira ‘yan Najeriya, “mutanen cikin bukkoki, wadanda idan su ka shiga Amurka ba su sha’awar komawa cikin bukkokin su.”

New York Times ta ruwaito cewa Trump ya furta wannan danyar magana ce a gaban wasu jami’an Najeriya wadanda aka boye sunayen su.

Sai dai kuma duk da wannan mummunan kalami Na Trump ga ‘yan Najeriya, kasar ba ta cikin jerin kasashen da aka haramta ta al’umar ta shiga Amurka.

Share.

game da Author