Wani ma’aikacin babbar asibitin koyarwa na jami’ar Fatakol UPTH jihar Ribas, Omosivie Maduka ya yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran bangarorin gwamnatin kan ware isassun kudade domin samun maganin kawar da cutar tarin fuka musamman yanzu da cutar bata jin magani.
Ya kuma yi kira ga malaman asibiti kan su tabbatar da cewa masu fama da wannan cutar na amfani da magungunan cutar yadda ya kamata.
” Kamata ya yi malaman asibiti su kula da masu fama da wannan cutar cikin farin ciki a duk asibitin da suke aiki sannan su tabbatar suna magana da marasa lafiya domin gano ko suna amfani da magani yadda ya kamata’’
Maduka ya ce hakan zai taimaka wajen rage yaduwar cutar musamman wanda baya jin magani.