SIYASA: Masari ya sallami kwamishinar Ilimin jihar

0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya sallami kwamishinan ilimin jihar Halimatu Idris.

Kakakin gwamnan Abdu Labaran wanda ya sanar da haka ya ce Masari ya sallami Halimatu ne saboda suna bukatan ‘yan siyasa su shigo fannin ilimi ganin cewa kwanan nan za a buga gangar siyasa.

Labaran ya Kara da cewa gwamnan ya mika godiyar sa ta musamman ga Halimatu saboda kyawawan aiyukkan da ta yi a fannin ilimin jihar.

Ya ce yana mata fatan alheri a duk abin da za ta yi nan gaba.

Share.

game da Author