Shekara biyu da rabi bayan cin zabe, Buhari za shi Kano

0

Duk da jihar Kano ce ta fi ba Buhari yawàn kuri’u fiye da sauran Jihohin Najeriya a 2015, da yawa daga cikin masu yin tsokaci a siyasa sun ce wannan ziyara ya yi daidai sai dai ya yi kusan latti.

Yau litini ne kakakin fadar shuagaban Kasa Garba Shehu ya sanar da shirin kai ziyara garin Kano da Buhari zai yi a wannan mako.

Garba ya zayyano wasu ayyuka da Buhari yayi wa mutanen Kano duk da bai Kai ga Kai musu ziyara ba.

Wasu da suka zanta da PREMIUM TIMES HAUSA daga Kano, sun ce suna maraba da wannan ziyara da Buhari zai yi, sannan suna yi masa fatan alkhairi.

Ismail Bala Rano, cewa yayi ” dama na san idan basu zo don su gode mana ba Kan zaben 2015, za su zo neman jama’a don 2019.”

Share.

game da Author