“Garken shanun da aka gani sun a kiwo a Fadar Shugaban Kasa, Aso Rock Villa cikin makon da ya gabata, shanun fadar ne, ba bakin shanu ba ne.”
Haka wani likitan dabbobi da ke fadar shugaban kasa, mai kula da asibitin dabbobin fadar ya bayyana.
Haruna Tanko ne ya bayyana haka, biyo bayan wani bidiyon da PREMIUM TIMES ta nuna a makon da ya gabata, inda aka nuna shanu na kiwo a Fadar Shugaban Kasa, a kan titi, kusa da kofar shiga gidan Mataimakin Shugaban Kasa, inda a lokacin su ka haifar sa tsaikon zirga-zirgar motoci masu wucewa.
Discussion about this post