Dan takarar shugabancin jam’iyyar PDP Uche Secondus ya duke Farfesa Tunde Adeniran da ake ganin shine kayar da zai iya makale masa a wuya a Zaben.
Adeniran ya sami kuri’u 200 da ‘yan burbudi Inda shi Secondus ya wawushe kusan duka kuri’un.
Duk da cewa duk ‘yan takaran da suka nemi kujeran shugabancin jam’iyyar daga yankin Kudu Maso Yamma duk sun janye, ana zaton sun janye wa dan uwan su ne daga yankin abin ba haka bane domin kamar yadda kuri’un suka nuna, bai sami komai ba daga Jihohin kudu maso Yamma.
Uche Secondus ya ya sami kuri’u 2000.