Kamar dai a kowace Majalisar Tarayya a duniya, ta Najeriya ma ba ta tsira daga hayaniya, hayagaga, cece-ku-ce, harkalla kai har ma da bahallatsa a 2017 ba.
PREMIUM TIMES TIMES ta kawo muku wasu bakwai da su ka fi saura yin kaurin suna a gurugubji da yamutsa gashin-baki walau a majalisar ne, mazabun su da Jihohin su.
1. DINO MELAYE: Sarka Uwar Rikici
Shi ne Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, kusan ya fi saura shiga tsomomuwa da kuma yin taratsi a 2017. Tun a cikin Maris hayaniya ta tirnike ilahirin kasar nan a kan zargin cewa Melaye ya kantara karyar kammala Jami’ar A.B.U Zaria.
Wannan wuta da ta rika cin Dino Melaye balbal, har ta nemi babbake shi, ba ta lafa ba har sai ranar da Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Farfesa Ibrahim Garba, ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa ya tabbatar da cewa Dino ya kammala jami’ar.
Sai dai kuma shekarar da Shugaban Jami’ar ya ce Melaye ya kammala, ba ta Yi daidai da shekarar da ya ke ikirarin ya tafi bautar kasa, wato NYSC ba.
Wannan ne ya sa ya fito da wata waka mai baiti daya tal, ‘Ajekun Iya,’ domin ya gwasale SaharaReporters, jaridar da ta fara fallasa cewa bai kammala jami’a ba.
Bayan wannan, Melaye ya sake shiga rikicin da ya sake yin kaurin suna, bayan da ‘yan mazabar sa 188,580 su ka rattaba hannun bukatar a yi masa kiranye.
A zaman yanzu wannan shari’a na kotu inda ta ke tafiyar hawainiya bayan da Dino ya garzaya kotu ya kai INEC wacce ke da alhaki da ikon yi masa kiranye.
Sai kuma cikin Oktoba, inda aka nuno wani hoton sa tare da wata matar da ba a san kowa ce ba. Shi ma wannan ya haifar masa da tsugune-tashi.
2. BUKOLA SARAKI: Faduwar Gaba Asarar Namiji
Bukola Saraki dai a cikin 2017 ya zama – shari’a ba ta sa gaban ka ya fadi.Kuma ya ya zama kura kun saba durkuso gaban alkali.
Katan-katanar Saraki, Shugaban Majalisar Dattawa ta samo asali ne daga tuhumar da CCT ta dade ta na yi masa, amma aka kori karar, ko kuma a ce kotun ta wanke shi cikin watan Yuni.
Amma kuma sai murna ta koma ciki a cikin watan Disamba, yayin da Kotun Daukaka Kara ta sake maida Saraki Kotun CCT domin ya amsa wasu tuhumomi 18 da ake zargin sa.
Shi dai Saraki babban laifin kantara karya wajen kin bayyana wasu kadarorin sa a lokacin da ya na Gwamnan Jihar Kwara.
Ana cikin wannan kuma sai sunan sa ya bayyana a cikin Tsomomuwar Paradise Papers, inda aka fallasa wani kamfani da ya ke darakta cewa bai taba biyan haraji ba.
Sunan kamfanin dai Tenia Limited, kuma a Tsibirin Cayman aka kafa shi don kada ya rika biyan haraji ba gwamnati.
3. BUKAR ABBA-IBRAHIM: Amfanin Zunubi Romo
Tabbas 2017 shekara ce da Sanata Bukar Abba, tsohon gwamnan jihar Yobe ba zai taba mantawa da ita ba. A cikin faifan watan Yuli ne wasu ‘yan tabare su ka fallasa wasu hotunan sa a cikin wani kazamin otal, yayin da ya ke sa wando, singileti da sauran suturun sa, mai yiwuwa bayan ya gama rakashewa da wasu mata biyu a lokaci daya.
Da ya ke har ma da bidiyo aka nuno, wannan bahallatsa ta janyo masa abin kunya da kiraye-kirayen a tsige shi.
Bukar shi ne mijin Karamar Ministar Harkokin Waje, Zainab Bukar Abba, wacce ta taba zama Mamba a Majalisar Tarayya har karo biyu.
Sanatan dai a lokacin da aka fallasa shi, ya ce tabbas shi ne, kuma babu ruwan wani da harkokin rayuwar sa, kowa ya je ya ji da harkar da ke gaban sa.
4. SHEHU SANI: Na Zaune Mai Ganin Kokawa
Kusan Sanata Shehu Sani ya shafe 2019 ya na rikici da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. Shehu da El-Rufai dai su biyun duk baubawan burmi ne – yayin da El-Rufai ke ganin cewa babu gwani sai shi, Shehu Sani kuma na yi wa El-Rufai kallon duk abin da ya yi ba daidai ba ne.
Ya zargi El-Rufai da tinjima jihar Kaduna cikin rijiyar bashi mai gaba dubu, wacce Allah kadai ya san shekarar da za a iya tsamo jihar daga ciki.
Baya ga alamomin da ya nuna cewa zai tsaya zaben 2019, ya fito ya soki lamirin tsayawar da El-Rufai ke neman sake yi a zaben 2019.
Cikin Satumba kuma ya ragargaji APCin Kaduna da ta amince El-Rufai ya sake tsayawa, ya na mai cewa, “APCin Kaduna ta sake jibga wa al’umar jihar dagwalon masana’antu.”
Shehu ya kuma caccaki gwamnan bayan ya kori malaman makaranta sama da 20,000.
Shi dai gwamnan ya ce Shehu ya sa kafar wando daya da shi ne, don ya ki nada ko da mutum daya daga cikin mutanen da Shehu ya turo ya na so a nada kwamishinoni.
5. ISA MISAU: Ciwon Ido Sai Hakuri
Sanata Isa Misau daga Bauchi, ya daura banten kokawa da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Ibrahim Idris, run daga ranar da ya zargi Shugaban ‘Yan sandan da yi masa karya wajen bada rahoton dalilin da ya sa Sanatan ya yi ritaya daga aikin dan sanda.
Daga nan shi ma sai ya zargi Sufeto Janar din da yin aure a asirce tare da wata jami’ar ‘yar sanda da ya ce hakan ya karya dokar aikin dan sanda.
Wannan rikici ya sa kwamitin Majalisar Dattawa ya sa gayyatar sufeton amma ba ya halarta. A ranar da ya je, ya shaida musu cewa shi ba abin da zai ce, domin magana ta na kotu.
6. ATAI AIDOKO ALI: Karshen Alewa Kasa
Shi ne Sanatan Kogi ta Gabas, wanda a ranar 18 Ga Disamba kafafen yada labarai su ka bayyana cewa kotu ta tsige shi daga Majalisar Dattawa. Shi kuma washegari ya tashi a zauren Majalisa ya ce babu inda alkali ya tsige shi yayin da ake zartas da hukunci.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta fallasa kwafen shaidun takardun shari’ar wadanda su ka tabbatar da cewa kotu ta tsige shi.
Amma har zuwa yau ya na kiran kan sa Sanatan Kogi ta Tsakiya. Ba mu san abin da za biyo gobe ba.
7. ALI NDUME: Jure Fari Sai Tofa
Sanata Ali Ndume ya hadu da fushin Majalisar Dattawa a lokacin da ya nemi a binciki Bukola Saraki da Dino Melaye a kan zargin da wasu jaridu su ka ce Dino ya yi fojare. Shi kuma Saraki bi-ta-da-kulli ya ke yi wa Shugaban Hukumar Kwastan, ba cika-aiki ba.
An dakatar da Ndume wata shida. Bayan cikar wa’adin, an yi kokarin kara masa wasu yawan kwanaki, amma ya garzaya kotu, kuma ya yi nasarar cewa hatta waccan dakatarwa da aka yi masa haramtacciya ce, don haka sai a biya shi dukkan albashi da alawus-alawus na watannin shida.
Discussion about this post