Ministan Harkokin Sufuri, ya shawarci ‘yan jam’iyyar APC da su kara rubanya kokarin da su ke yi ga al’umma, sannan su kara kusantar da kan su ga Allah domin yin nasara a kan PDP a zaben 2019.
Rotimi Amaechi ya yi wannan kalamin ne yayin da aka gudanar da bikin cikar shekara goma da Allah ya ba shi nasarar zama gwamnan jihar Rivers ta hanyar hukuncin da Kotun Koli ya yanke a lokacin.
Amaechi dai ya yi wa wadanda suka taya shi murna a cikin Cocin Evangelic na Fatakwal tariyar abin da ya faru da shi a wancan lokaci, a cikin 2007. Ya ce Allah ya goya masa baya, a lokacin kowa ya kware masa baya.
Da ya juyo kan ‘yan siyasa da abokan sa, ya yi mamakin ganin yadda da yawan su wadanda ya taimaka suka zama wani abu a rayuwa da wadanda ya tsamo a cikin kwatami, ya suturta su, amma a yau su ne manyan masu gaba da shi.
Daga nan kuma ya shawarci matasa da su rika taimakon mutanen da ke kewaye da su idan har Allah ya dora su a kan mulki.