Rikici ya kaure tsakanin Fulani da Manoma a kauyukan Numan

0

Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka ana can ana hargitsi a wasu kauyuka biyu da ke kilomita 10 da garin Numan na jihar Adamawa.

Fadan dai ya tashi ne tsakanin Fulani makiyaya da kabilun Bachama da ke kewayen Numan.

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Adamawa ta tabbatar da afkuwar rikicin, amma ta ce a yanzu komai ya lafa, domin an tura jami’an tsaro, ciki kuwa har da sojoji zuwa kauyukan. Haka dai Othman Abubakar, kakakin rundunar ya bayyana.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kashe mutane da yawa, yayin da da dama kuma musamman mata da kananan yara su na ta tserewa daga yankin.

Wannan hari dai an yi zargin hari ne na ramuwar gayya ko a ce daukar fansa da Fulani suka kai kauyen Dong da ke cikin Karamar Hukumar Demsa, bayan sabani da aka samu tsakanin manoma da Fulani makiyaya.

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce ba zai iya tabbatarwa ko harin na da alaka da na daukar fansa ba ko a’a.

Wani dan kabilar Bachama da ya tsira da kyar mai suna Gregon Daniel, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kona gidan su kurmus a kauyen Dong.

“Sa’o’i kadan da suka gabata ne suka dira cikin kauyukan, suka rika kashe na kashewa, su na banka wa gidaje wuta.”

“Yanzu maganar nan da na ke yi da kai ana can ana fada, amma wasu musamman mata da yara sun tsere sun buya cikin daji.” Inji Daniel.

Share.

game da Author