Tilas mahukuntan Najeriya su tabbatar da cewa sun yi adalci, an bayyana gaskiya kuma an biya diyyar ilahirin mabiya Shi’a sama da 350 da aka kashe a garin Zaria, Arewacin Najeriya, a cikin Disamba. Haka Kungiyar Jinkai ta Duniya ta bayyana.
Tun da aka yi kisan, har yau ba a ce ga wanda ke da alhakin wannan aika-aika ba, yayin da iyalan wadanda su ka bace har yau su n a zaman jiran dangin su da har yau ba a san inda su ke ba. Kungiyar Jinkai ta duniya ta samu kai ziyara a Mando, inda aka yi wa daruruwan wadanda aka kashe kabarin-bai-daya, amma dai har yau ba a tone kabarin ba, ballantana ta samu damar kididdige su.
Amnesty ta ce yanzu kisan jama’a a kasar nan ba a bakin komai ya ke ba, duk kuwa da ya kasance an san cewa keta hakkin dan Adam ne.” Haka Daraktan kungiyar na Najeriya, Osai Ojigbo ya bayyana.
“Binciken mu ya nuna cewa yawan jama’ar da aka kashe sanadiyyar rikicin da ya barke tsakanin mabiyan Shi’a da kuma sojojin Najeriya, ya faru ne saboda amfani da karfin tsiya da sojoji suka yi, wanda tilas ne a binciki kisan.”
Tsakanin 12 Ga Disamba zuwa 14 Ga Disamba, jami’an tsaron Najeriya sun kashe daruruwan fararen hula, ciki har da mata da kananan yara, sannan kuma suka kama sama da 300.
Wadanda aka kashe dai babu takamaiman adadin su, yawan su zai iya zarce wanda gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar na gawarwaki 347 da kan ta cewa ita ce ta dauki nauyin hanzartawa a rufe su.
“Tun tuni ya kamata a ce an bar wani kwamitin bincike mai zaman kan san a kasa da kasa ya zo ya yi bincike domin a san makomar ‘yan uwan su da har yau babu su kuma babu labarin su tun daga ranar 12 Ga Disamba, 2015.
“Sannan kuma ya kamata Ministan Shari’a kuma Attoni Janar na Najeriya ya bayar da umarni a tone kabarin, a san adadin wadanda ke ciki, sannan a hukunta dukkan wadanda ke da hannu a wannan kisa daidai irin wanda suka aikata.”
Har yau dai Jagoran tafiyar IMN, Sheikh Ibraheem ElZakzaky da matar sa sun a tsare ba bisa ka’idar shari’a ba, duk kuwa da cewa Babbar Kotun Abuja ta ce a sake su.
Discussion about this post