Babban limamin cocin St.Bartholomeus, Ali Lamido ya ce duk da yawan matsalolin da kasar nan ke fama da su kamar su Boko Haram, rikicin dake tasowa tsakanin makiyaya da manoma, kungiyar IPOB da sauran su mutanen Najeriya na kishin juna da son Zama tare
Ya fadi hakan ne a taron cika shekaru 20 da kafa dayosis din cocin da aka yi a Zariya jihar Kaduna.
Ya ce duk da cewa wasu mutane na kokarin ganin kasar nan ta rabu, yin hakan ba shine zai kawar da matsalolin da kasan ke fama da su ba.
Ya kuma yi kira ga mutanen da ke son a canza fasalin kasar nan da wadanda basa son hakan adawa da hakan su tabbata duk abin da zasu yi ba zai wargaza gadin Kan Kasar nan ba.
Bayan haka Lamido ya jinjinawa aiyukkan raya kasa da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ke yi a fanonin ilimi, kiwon lafiya, samar da aikin yi da sauransu a jihar.
” A ra’ayi na kamata ya yi gwamnati ta inganta kwarewar malamai ta hanyar basu horo sannan ta mayar da malaman da suka gaza wasu ma’aikatu a jihar.”
Daga karshe ya yi kira ga gwamnati da ta kara samar da tsaro a manyan fitina kasar nan domin kawo karshen sace sacen mutanen da ake yi a hanyoyin mu.