Duk wani masoyin jam’iyyar PDP a kasar nan yana nan ya na jiran ko yaya zata kaya tsakanin ‘yan takaran da suke so su zama shugabanni a jam’iyyar.
Bayan kurda-kurda da akayi ta yi tun daga daren jiya zuwa yau, yan takara musamman na wanda zai shugabanci jam’iyyar suke ta hadewa domin ganin ba su rarraba kuri’un su ba wajen ganin ba wanda bai cancanta ba ne ya lashe zaben.
Duk ‘yan takaran da suka fito daga yankin kudu maso yamma sun hakura da takaran inda suka tsayar da Farfesa Tunde Adeniran dan takaran su.
Ko da yake basu ambata cewa wai shi dinne zasu zaba ba alamu ya nuna cewa lallai hakan za suyi.
Sauran yan takaran Raymon Dokpesi da Uche Secoundus duk sun fito daga yankin Kudu Maso Kudu ne.
A wani hira da tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja yayi kafin zaben ya bayyana cewa dole ne su hada kansu yan kabilar ‘yarbawa wuri guda su tsaida dan takara daya idan suna so su ci wannan zabe.
Yace ‘yan Arewa sun roke su da su samar da dan takara daya domin su mara masa baya.
Yanzu dai masu yin fashin baki a harkar siyasa sun tsokata cewa wannan zabe dai zai iya zama nasara ga jam’iyyar ko kuma ya sake tarwatsa jam’iyyar idan ba’a yi takatsantsan ba.
Yankin kudu maso kudu suna korafin cewa lallai dan yankin ne ya kamata ya jagoranci jam’iyyar ganin cewa kaf yankin nasu, PDP ce ke mulki a jihohin su, Saboda haka sune suka cancanci rike jamiyyar.
Su kuma yankin Kudu maso Yamma na ganin lallai ba dan yankin ne kawai mafita ga PDP ganin cewa jam’iyyar APC ce take da karfi a yankin. Suna ganin idan dan yankin ya zama shugaban jam’iyyar zasu iya samun dan tasiri a yankin zuwa zaben 2019.
Yanzu dai duk wanda ya zama shugaban jam’iyyar dole ya maida hankali wajen hada kan ‘yayan jam’iyyar domin ganin ta samu nasara a zabuka masu zuwa ganin cewa ita kan ta jam’iyya mai mulki wato APC tana tangal tangal ne inda talakawa na ta korafi kan wahalar rayuwa da suke fama dashi da rashin tsaro ya ya addabi mutane.
Discussion about this post