PDP ta zargi APC da yinkurin hargitsa mata gangamin jam’iyya

0

Jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa akwai wasu “masu wuce-makadi-da-rawa” a cikin jam’iyyar APC na ta kulle-kullen hargitsa taron gangamin da jam’iyyar za ta yi Asabar mai zuwa a Abuja.

Babban Sakataren Jam’iyyar na Kasa na riko, Dayo Adeyeye ne ya yi wannan tsinkayen a wani taron sa da manema labarai a Abuja.

Adeyeye ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi bincike sannan kuma ya tabbatar da cewa ba a hargitsa gangamin PDP ba.

Ya ce babu ruwan shugaban kasa cikin wannan makarkashiyar da ake shirin kulla wa PDP, amma akwai wasu ‘yan jam’iyyar sa da ke shirin kawo rudani a wurin.

“Saboda mu na da majiya mai makama cewa akwai wannan yinkuri daga cikin wasu jami’an gwamnatin APC cewa za su tarwatsa taron.

“Saboda sun tabbatar matsawar muka yi gangami salun-alum, to mulkin APC ya zo karshe kenan.”

A karshe ya yi gargadin cewa to ya kamata shugaba Buhari ya sani, hargitsa gangamin PDP tamkar hargitsa dimokradiyyar kasar nan ce.

Share.

game da Author