Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ya na goyon baya 100 bisa 100 na Uche Secondus ya zama shugaban jam’iyya na riko.
A ranar Asabar ne PDP za ta yi gangami domin zaben shugabannin jam’iyya na kasa.
Secondus wanda dan asalin jihar Rivers ne, ya na ta fadi-tashin ganin ya zama shugaban jam’iyya mafi girma daga cikin jam’iyyun adawar kasar nan.
Wike ya ce a matsayin Secondus wanda ya taba rike shugabancin PDP na riko, shi ne mafi cancanta a yanzu ya jagorance ta.
A cikin wata takarda da kakakin Wike ya sa wa hannu, ya ce Secondus ne kadai daga cikin ‘yan takara wanda ya fito daga cikin jihar da PDP ke mulki a kasar nan.
Ya ce babu wani dan takara mai bakin fada a ji a siyasar jihar sa, sai Secondus.
Wike ya ce kafin ya yi bayanin sa, a matsayin sa na dan siyasa sai da ya yi nazarin dukkan ‘yan takarar tare da yin nazarin yanayin da za a shiga.
Ya ce ya na da yakinin kashi 90 bisa dari na masu zabe, Secondus za su zaba.
Sai ya ce ya Fita daga cikin kwamitin tsara gangamin ne domin kawai ya yi wa Secondus kamfen har ya samu nasara.
A karshe ya ce karya kawai wasu ke ta yadawa wai Secondus na da matsala da EFCC.
Wike ya ce Secondus bai ci buzun kura ba, ballantana a ce ya yi aman gashin kura.