A yau Talata ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kai ziyara kauyan Numan dake jihar Adamawa.
Ya kai wannan ziyara ne domin yin ta’aziyya da mutanen kauyukan Numan din da suka rasa ‘yan uwan su sanadiyyar rikicin yaki ci yaki cinyewa a tsakanin Fulani da Manoma a yankin.
Da sauka garin Yola, Osinbajo ya kai ziyarar ban girma
ga Lamido Adamawa Barkindo Mustapha inda suka tattauna tare da sauran sarakunan gargajiya na garin Numan din.
Bayan sun kammala Osibajo ya kai ziyara kauyukan Numan inda ya gana da masu unguwannin yankin.
Osinbajo ya ce gwamnati ta yi ziyarar gani wa ido ne domin ganin yadda za a kawo karshen wannan rashin jituwa da yaki ci yaki cinyewa.