Ban san dalilin da ya sa magoya bayan jam’iyyar APC su ka rufe idanu daga kallon matsalar da ke gaban su ba, su ka koma su na yi wa jam’iyyar PDP dariya, don kawai ta samu rashin jituwa a wurin zaben shugabannin ta a Abuja, wurin Gangamin 2017 da ta gudanar.
Babban abin da jam’iyyar APC ta yi wa ‘yan Nijeriya ci-da-buguzum da shi, a lokacin yakin neman zabe, shi ne matsalar tsaro. A lokacin Book Haram ta kusa mamaye Arewa, ko ma a ce ta mamaye din, sai dan abin da ba a rasa ba.
An zabi gwamnatin APC domin magance tsaro da kuma kakkabe cin hanci da rashawa. Kuma da wannan dalilin ne ya sa aka kayar da Gwamnatin PDP ta Goodluck Jonathan, domin ana yi masa kallon ya yi wa harkar Boko Haram rikon-sakainar-kashi.
Hawan Gwamnatin Muhammadu Buhari an samu nasarar karya fukafikan Boko Haram, ta yadda ba su iya faffaka su tashi tun daga Barno su rika dora sauran jihohin Arewacin kasar nan – in banda Yobe da kuma Adamawa da ke makwabtaka da Barno.
Amma duk wani wanda ya yarda da kalaman da Gwamnatin APC ke yi cewa wai sun gama da Boko Haram, to ya na yaudarar kan sa ne kawai. Duk yadda ka kai son Buhari, ba zai yiwu ka shiga Barno ko Yobe da Adamawa ka ce babu Boko Haram ba.
Wani Bincike Na Musamman da wata jaridar kasar nan ta gudanar kwanan baya, sun kawo cikakkun hujjoji cewa Boko Haram ta kashe mutane 1008, daga ranar da Shugaba Buhari ya ce an kakkabe Boko Haram zuwa ranar da binciken na su ya fito.
A yau ko gobe, idan za ka tambayi da yawan matafiya, za ka ji sun ce maka sun fi jin tsoron haduwa da masu garkuwa da mutane fiye da ‘yan fashi. Sai ta-baci dan fashi ke kisa. Abin da ya fi so shi ne ka ba shi kudin ka, ka yi gaba, shi ma ya gudu.
Amma masu garkuwa da mutane kudin da kai da dangin ka ma ko a banki wani ba ku taba ganin su ba, su za a nemi a ce iyalin mutum ko ‘yan uwan sa su bayar, kafin a sake shi.
Abin takaicin shi ne da an dan yi wani harrr, an ce an kara jami’an tsaro a kan titin, sai kuma ka ji an sake yin garkuwa da wani. Firgicin d ke cikin wannan fitina kuwa shi ne, a farkon fara garkuwar, yawanci duk rikakkun barayin da suka isa ne ke tare hanya. Amma a yanzu akasari duk kartin kauye ne, kuma Hausawa da Fulani, wadanda ko karatun firamare wasu ma ba su samu damar zuwa sun yi ba.
Game-garin magoya bayan APC ido-rufe fa ba su dauki wannan matsala a matsayin wata matsala ba, tunda Buhari ne ke mulki ba Jonathan ba.
DAGA BOKO HARAM ZUWA GARKUWA DA MUTANE
Babban abin da Gwamnatin APC ta fi bugun gaba da shi a nasarorin ta, shi ne tsaron da ta ke cewa ta samar a Arewacin kasar nan.
To sai dai kuma wata babbar barazana ga wannan Gwamnatin ita ce matsalar sace mutane, ana yin garkuwa da su. Ba a Gwamnatin APC aka fara ba, amma ya fi kamari, yawaita da kuma addabar jama’a a wannan lokaci da Buhari ke mulki.
Duk wani dan Arewa, ko mai zuwa Arewa zuwa ko daga Kaduna, Kano, Daura, Katsina, Bauchi, Potiskum, Damaturu, Maiduguri, Sokoto, Gusau, Zaria da Kebbi da sauran garuruwa, babban tashin hankalin da ya ke tunani, shi ne kada Allah ya sa a sace shi a tsakanin Kaduna zuwa Abuja, ko Jos zuwa Abuja, ko kuma Birnin Gwari zuwa Kaduna.
Daga hawan mulkin Buhari zuwa yau, Allah kadai ya san yawan mutanen da aka yi garkuwa da su, walau babba ko yaro, masu mulki da cikin talakawa. Maimakon a ce ana samun nasarar shawo kan abin, sai ma kara yawaita da ya ke yi.
Ina gudun duk ranar da talaka ya gane cewa zancen gaskiya Boko Haram na nan, ba a ga bayan su ba, kuma kullum su na fafata yaki da sojojin mu. Sannan kuma talaka ya gane cewa sama da shekaru Gwamnatin APC ta kasa magance matsalar garkuwa da mutane, to zai iya canja tunani a 2019.
Ai dama irin wannan ce ta yi wa Gwamnatin Jonathan tadiya, ya girde ya fadi a zaben 2015. Matsalar Boko Haram ta hana a ga ayyukan alherin da ya yi a kasar nan masu yawa, ciki kuwa har da gina jami’o’i a yawancin jihohin kasar nan.
Idan Gwamnatin APC ta kasa. magance garkuwa da mutane, da me za ta yi kamfen a Arewa? Idan ta kasa magance kashe-kashen Fulani da kabilu manoma a Filato, Nassarawa, Benue da Adamawa da Taraba, to da me za ta yi kamfen a yankin Arewa ta Tsakiya, wato Middle Belt?
Gyara kayan ka dai bai zama sauke-mu-raba ba.