Dawowar hare hare da ‘yan ta’adda suke kai wa masallatai na da matukar tada hankali, musamman yadda wannan al’ada ta zamo ruwan dare a fadin duniya ga baki daya.
A Jumma’ar da ta gabata muka samu wani labari daga lardin Sinai dake kasar masar, yadda ‘yan bindiga suka kutsa cikin masallaci daidai lokacin da ake gabatar da sallah suka kuma budewa masallata wuta, inda rahotanni tashar talbijin ta kasar Amurka – CNN ya rawaito cewa sama da mutane 305 ne suka rasu da dama kuma suna asibiti.
Irin wadannan hare hare a masallatai ba sabbin abu ba ne a kasar nan, musamman idan muka dubi yadda tun 2009 lokacin da aka fara rigimar Boko Haram irin wannan ta’addancin kan masallata ya mamaye arewacin kasar nan. Daga Maiduguri, Yobe, Adamawa, Jos da Kano.
A 2014 ne babban masallacin fadar Sarkin Kano ya samu nasa rabon na irin wannan ta’addanci yadda sama da masallata 200 suka rasu a take, wasu da yawa kuma suka karasa a asibitoci da gidajen su.
A masallacin ‘Yan Taya dake Jos shi ma haka aka samu mutuwar sama da mutane 70, yayin da ‘yan ta’ada suka afkawa masallacin a daidai lokacin da ake gabatar da tafsiri cikin azumin watan Ramadan.
Bayan afkuwan irin wadannan hare hare kan dakin Allah, hukumomi na masallatai sun dauki matakai masu yawa wajen kariya da kuma dakile duk wata baraza da ka iya afkuwa a kan masallatan nasu, musamman ta yin amfani da ‘yan agaji wajen binciken duk mai shigowa masallaci ko da kuwa limami ne shi, da kuma tabbatar da cewa babu wani kunshi da ke harabar masallacin wanda ba a san da zaman sa ba.
Tabbas ire iren wadancan matakai sun taimaka sosai wajen dakile irin wadannan hare hare a kan masallatai. Shi ya sa a yanzu zai yi wuya ka je shiga masallaci ka ga wani dan agaji zai bincike ka saboda a tunanin mu lokacin irin wannan binciken ya wuce.
Kwatsam ranar litinin 30 ga watan Oktoba sai ga labari an kai hari kan masallata a garin Maiduguri daidai lokacin da suke gabatar da sallar asuba, inda fiye da mutane 15 suka rasu kuma da yawa aka garzaya da su asibiti. Ba a gama numfasawa daga wannan rashi na Maiduguri ba sai ga wani mummunan hari a garin Dazal dake karamar hukumar Mubi a jihar Adamawa, fiye da mutane 50 suka rasu.
Alamu na nuni dacewa yin biris da mutane suka yi wajen kare masallatansu kamar yadda suka yi a baya na taimakawa wajen samun nasara ga ayyukan wadannan ‘yan ta’adda, hukuma kadai ba za ta iya bayar da dukkan tsaro ba, musamman cikin wuraren ibada. Kamar yadda irin waccan halayyar ta kisan gilla ta faro daga gabashin kasar nan to, yanzu ma ta sake bullowa. Bai kamata mu bari har sai ta cim mana kafin mu dauki matakai ba.
Abdulmajid Lawan Sani Waziri mazaunin garin Jos ne Jihar Filato
Discussion about this post