Mutane 1,070 suka mutu a hadarin mota tsakanin Yuli da Satumba

0

Akalla mutane `1,070 ne suka rasa rayukan su sanadiyyar hadarin mota tsakanin watan Yuli da Satumba a kasar nan.
Hukumar Kididdigar Bayanai ta Kasa ce ta bayyana haka.

Hakan nan hukumar ta yi nuni da cewa a cikin kwanaki 92, daga 1 Ga Yuli, zuwa 30 Ga Satumba, akalla a kullum mutane 11 na rasa rayukan su kenan.

Hukumar Kididdiga ta kara da cewa bayanan da suka tattara kuma suka tantance a wadannan watanni, ya tabbatar da cewa akasarin wadanda suka rasa rayukan na su duk magidanta ne, ba kananan yara ba.

Rahoton ya ce daga cikin wadanda suka rasa rayukan su 1,070, kusan mutane 981 duk magidanta ne, sai kuma 89 su ne adadin kananan yara.

An rasa rayukan maza 815 sai mata 255, yayin da rahoton ya ce an samu faruwar hadurra har 2,478 a cikin wadannan watanni uku.

Rahoton dai ya danganta yawan hadurran da gudun famfalakin da direbobi ke yi da sauran su.

Daga cikin wannan yawan hadurra har 2,478 da aka lissafa a sama da suka auku cikin watanni uku, an samu kuma wadanda suka ji raunuka har mutane 6,803.

Share.

game da Author