Muna neman Taimako da agaji – ‘Yan Kasuwar Panteka dake Kaduna

0

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Panteka dake Tudun-Wada Kaduna Suleiman Shehu ya yi kira ga maso hali da su taimaka wa ‘yan kasuwar Panteka da ke Kaduna da suka yi hasarar dukiyoyin su a dalilin gobara da ta lashe sama da shagunanan katako 700.

Ya bayyana da haka ne a ziyarar da Galadiman Ruwan Zazzau Ja’afaru Sa’ad yayi wa kasuwar domin jajanta musu kan gobaran da aka yi.

Shehu ya ce gobaran ta fara ne a kasuwar katakai da misalin karfe 1 na daren Juma’a inda ta kona katakan da zai kai tirela 100 sannan da na’urori 200.

Ya ce sanadiyyar gobaran matasa 30,000 sun rasa hanyar samun abincin su.

Shehu ya ce koda yake gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I, wakilan hukumar bada agajin gaggawa na kasa da na jihar Kaduna (NEMA da KEMA) sun ziyarce su amma suna kira ga gwamnati da sauran mutanen Najeriya da su kawo musu agaji da taimako.

Share.

game da Author