Mun Kashe naira Biliyan 2 wajen gina magudanar ruwa a Katsina – Masari

0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kashe naira biliyan 2 wajen gina magudanar ruwa a fadin jihar.

Masari ya fadi haka ne da ya ke karbar bakuncin wasu ‘yan siyasa da suka kawo masa ziyara fadar gwamnati ranar Litini.

” Gwamantin mu ta yi shekaru biyu tana gina magudanar ruwa daga Sabuwar-Unguwa zuwa gadan Adeleke Bridge zuwa Tudun-Natsira da Kofar-Sauri.

” Sauran wuraren da muka gina magudanar ruwan sun hada da Kofar-Kwaya da Kofar-Kaura, mun kuma gina magudanar ruwa daga fadan sarkin Katsina zuwa babbar asibitin jihar.”

Ya kuma ce sun gina shingen bayan gari a jihar sannan sun kange wasu kududdufai da suke yawan kawo matsala wa mazauna garin.

Daga karshe Mannir Yakubu wanda ya jagoran ci tawagar da suka kawo wa gwamnan ziyara ya mika godiyar sa na musamman ga gwamna Masari saboda gyara asibitocin da gyara wasu makarantu da ya yi a jihar.

Share.

game da Author