MULKI DA SIYASA A NAJERIYA: Yadda Fulani suka yi wa Hausawa rata daga 1800 zuwa yau -Kurawa

0

IBRAHIM ADO KURAWA ya taba zama Daraktan Hukumar Bincike da Tattara Bayanai ta Jihar Kano, a lokacin mulkin tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau. Duk da cewa ya yi ilmi mai zurfi ne a fannin kimiyya, Kurawa ya tsunduna cikin duniyar bincike da tarihi, har ya zama kwararren da a yau ake dogaro da bayanan sa ko sakamakon da ya binciko.

A wannan Tattaunawa ta Musamman da ya yi da PREMIUM TIMES HAUSA, ya yi bayanai masu dama a kan yadda Fulani su ka yi wa Hausawa rata mai yawa a sha’anin mulki, shugabanci da siyasa. Bai tsaya a nan ba, sai ma da ya kawo asali, tushe da salsalar tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Marigayi General Murtala. A sha karatu lafiya.

PTH: Kai da ka karanci ilmin kimiyya mai zurfi, me ya kai ka tsunduma cikin bincike-binciken al’amurran ko ababen tarihi?

KURAWA: Abin da ya ja har na tsunduma a sha’anin bincike-bincike na tarihi, shi ne, kamar shekaru 30 da su ka gabata, sai na fahimci mutane na ikirarin wai tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Murtala Mohammed daga Auchi ta cikin tsohuwar jihar Bendel ya fito, a can ne asalin sa. Wannan abu kuwa ya yi matukar muni sosai, domin ni da marigayi Janar Murtala duk daga tsatso daya muka fito.

Daga nan sai na fara binciken tushen mu da asalin mu domin na fito da komai kowa ya karanta. Na yi binciken tushen asalin mu, tarihe-tarihe, littatafan Larabci da rubuce-rubuce na Larabci da sauran su dai. To daga nan na fara shawa’ar bincike har na yi zurfi a ciki sosai.

PT: Ya kusancin ka ya ke da marigayi Murtala?

KURAWA: Da kaka na da kakan Murtala kakan su daya. Bari ka ji yadda abin ya ke tun asali. Muhammad Zangi shi ne mahaifin kakan Murtala. Shi kuma Zangi ya yi Babban Alkali a Kano a zamanin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. A cikin 1868 ya rubuta wani littafi mai suna Attaqidil Akbar. Ya na da kyau kuma a sani cewa shi Zangi din nan, ya na daya daga cikin manyan almajiran Sarkin Musulmi Muhammadu Bello a cibiyar ilmin sa ta Silame.

Lokacin da ya zama Babban Alkalin Kano, sai Sarkin Kano na lokacin, Abdullahi Maje-Karofi ya umarce shi da ya rubuta littafi mai kunshe da tarihin yadda jihadin Kano ya wanzu, domin ‘yan baya su san hakikanin yadda abubuwa su ka faru a lokacin.

To dalili kenan aka yi ittifaki cewa ruwayar Muhammad Zangi kan yadda jihadin Kano ya tabbata, ita ce ruwaya mafi inganci, bayan ta Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. Wannan Muhammad Zangi din shi ne ya haifi Sulaiman, shi kuma ya haifi Muhammad Riskuwa, shi kuma Muhammad Riskuwa shi ne mahaifin Murtala.

Ni da Murtala jinin mu daya, domin ni ma Muhammad Zangi shi ya haifi Shehu, shi kuma Shehu ya haifi Muhammad, shi kuma Muhammad ya haifi Ado Hakimin Karamar Hukumar Tarauni na yanzu. Ado kuma shi ya haife ni. Ka ga ashe kenan ni da Murtala duk daga tsatson Zangi muka fito.

Dalilin wannan bincike da na yi ne sai da ta kai ni ga fassara littafin Zangi daga Larabci zuwa Turanci a cikin 1989. Na shaida maka fa Zangi ya rubuta littafin a cikin 1868. Shehu dan Muhammad Zangi, wanda shi ne kaka na, Sarkin Kano Tukur ne ya kashe shi a lokacin Yakin Basasar da aka yi a Kano kafin zuwan Turawa.

Shi kuma dan’uwan sa Sulaiman, wanda shi ne Kakan Murtala, ya na da kusanci da Sarkin Musulmi Attahiru, kamar yadda wancan littafi ya nuna. Shi ne ma Babban Alkalin Kano a lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka ci Kano. Bayan Turawa sun kama Kano, sai suka cire shi, aka nada Malam Gidado.

PT: Ganin yadda ka koro da wannan bayani tiryan-tiryan, masu karatu za su kagara su ji shin shi Muhammad Zangi, dan asalin wace kabila ce kenan?

KURAWA: Mohammadu Zangi ya fito ne daga kabilar Fulanin Gyanawa. Su kuma Gyanawa sun fito ne daga tsatson Fulani Jallubawa. Ka san Fulani sun kasu kashi daban-daban. Akwai Sullubawa, Ba’awa, Gyanawa, Toronkawa, Danejawa da sauran su. To su kuma Gyanawa sun shigo ne daga Futa Toro, suka zauna a Bargami, daga can suka fantsama har nan wajajen a tsakanin shekarun karni na 1500.

Ka ga na ma manta ban shaida maka ba tun da farko. Mahaifin Zangi mai suna Salihu almajirin Usman Danfodiyo ne. Akwai wani littafi da dan’uwan sa mai suna Abdullahi Alkanawy ya rubuta. Sunan littafin Addawa’ir. Akwai bayanin littafin da cikin littafin da Farfesa Murray Last ya rubuta mai suna ‘Sokoto Caliphate’, wato Daular Usmaniyya.

PT: Wane irin kusanci ka yi da Murtala kafin a kashe shi ya na shugabancin Najeriya?

KURAWA: Lokacin da aka kashe shi, ni ina firamare ai. Amma abin da kawai zan iya tunawa shi ne duk lokacin da ya zo Kano, ya kan ziyarci kanuwar mahaifin sa, wato gwaggon sa A’isha har gidan ta. To a lokacin ita gwaggon tasa ce ke rike da ni, a hannun ta na ke. Ka ga sai na ce maka ya na zuwa gidan mu kenan.
PTH: Idan mu ka yi duba ga tahirin yadda Fulani suka kafa daula a kasar Hausa tsakanin 1800 zuwa 1900, ana ganin cewa wannan fifiko har yanzu ya na tasiri idan aka yi la’akari da yadda shugabanci ke tafiya har yanzu a Najeriya. Kai ya ka ke kallon abin?

KURAWA: To ai sai mu kalli tarihin kan sa domin mu fahimci yadda al’amurra su ka rika faruwa. Ba wai haka kawai saboda ka na Fulani ba ne za ka iya zama shugaban kasa ko wani abu ba. Ba haka abin ya ke ba. Da farko su dama Fulanin da suka kafa Daular Usmaniyya kowa ya san masu ilmi ne, masana kuma malamai ne. Su ne ma su ka shimfida ilmin a wannan yanki na mu. A Kano misali, lokacin da Fulani suka fara zuwa cikin karni na 14, ai duk mashahuran malamai ne.

Kasancewar mutum na da ilmin addinin musulunci a lokacin, hakan ta ba shi damar neman dimbin sani sosai. Dalili kenan ka ga duk wadanda suka samu damar rike shugabanci na mulki, masana ko malamai ne.

Sannan kuma shi kan sa jihadin Shehu Usmanu idan ka kalle shi, za ka ga wani juyin-juya-hali ne na masu ilmi. Ko a lokacin jihadin, akasarin Fulanin da ke zaune a kasar Hausa wadanda almajiran Shehu Usmanu ne, ai duk malamai ne.

Amma kuma mu fahimci cewa su manyan mukarraban Shehu Danfodiyo fa sun yi wani muhimmin abu wanda ya taimaka wajen hada kan Arewacin kasar nan. Wato sun fifita ko sun maida harshen Hausa a matsayin yaren magana da kuma rubuce-rubuce. Yawancin littattafan su da Hausa aka rubuta su.

Ka ga hakan ya yi tasiri, domin a yau yawancin Funanin da ke zaune a garuruwa da birane duk ba su magana da Fulatanci, sai da Hausa. Na tabbata Sarkin Musulmi na yanzu da Sarkin Kano duk ba su magana da Fulatanci, sai da Hausa ko Turanci.

Shi kan sa Marigayi Sardauna ai Hausa ya ke yi da Turanci, ba Fulatanci ba. Ka ga kuwa ai duk Falani ne.

Sannan kuma, wani abu muhimmi da ya kamata ka duba shi ne, ita ma Hausar ai ta mamaye komai. Yaren ta ne ake mu’amala da shi, tsarin suturar ta, abincin ta kai hatta tsarin sarautar gargajiya ma duk na Hausa ake yi. To mene ne kuma bambancin tsakanin Hausawa da Fulani a yanzu? Sai dai kawai idan zance ya tashi wannan ya ce kakanni na Fulani ne, wancan kuma ya ce kakanni na Hausawa ne. Don haka ka ga kenan babu wani karfa-karfa da a yanzu za a ce Fualani sun yi wa Hausawa.

PT: To amma ba ka kallon yadda Fulani suka yi wa Hausawa rata a wajen ilmin zamani? Ko ba su yi musu ba? Ko a sha’anin mulki, Janar murtala Bafulatani ne, haka Shehu Shagari da ’Yar’Adua da Muhammadu Buhari. Sannnan kuma yawancin ministocin Jamhuriya ta farko kai har zuwa yanzu na Arewa, Fulani ne suke da rinjaye kan Hausawa. Ko gwamnonin jihohi ma na farar hula tun daga farko har zuwa yau, Fulani ke da rinjaye sosai. Kamar dai akwai wani abu a boye ko?

KURAWA: To tunda har ka kawo wannan maganar, bari ka ji wani abu. Batun ilmi da ka fara yi, idan ka kalli lamarin, za ka ga cewa shi dama Bahaushe tun cikin karni na 19 har zuwa lokacin da Turawan mulki su ka shigo, bai damu da neman ilmi ba. Kai dai bar shi ga noma da fatauci kawai. Yayin da su kuma Fulani su ne malamai, su kuma ke karatun sauran fannonin ilmin musulunci.

Wannan sai ya bai wa Fulani damar karkata zuwa ga ilmin zamani lokacin da Turawa suka shigo. Dama kuma shi kan sa ilmin zamanin a kasar Hausa dai ai ta hannun sarakunan gargajiya ya shigo, wadanda Fulanin ne, su ke mulki.

Turawan Mulki sun rika tilasta wa sarakuna da sauran masu mulkin gargajiya su sa ‘ya’yan su makarantar boko.

Dalibin farko a makarantar Gidan Danhausa a Kano, Bafulatani ne, sauran ma duk Fulanin ne duk ‘ya’yan masu mulki. Kai ko a firamare ma duk ‘ya’yan sarakuna da masu mulki ne su ka fara shiga, ko aka fara dauka.

To haka abin ya rika tafiya. Ka ga ashe duk wanda ya kammala karatu, shi ma a gaba zai sa na sa yaran. Wadanda ba su fara karatu ba a lokacin, to za a dauki lokaci mai tsawo kafin su cimma tazarar da aka yi musu.

Bahaushen farko da ya fara karatu a Makarantar Middle ta Kano shi ne Musa Iliyasu, ina jin a cikin 1939 ko 1940 aka sa shi makarantar. Malam Aminu Kano ma ya riga shi shiga kenan, domin shi tun a wajajen 1936 ya shiga Makarantar Katsina. To sai ka duba da kyau, Bello Kano, Dokaji, Ahmadu Matidan, Sani Dan Ciroma duk sun riga Musa Iliyasu shiga da shekaru kusan 20. Domin su tun a 1921 or 1922 su ka shiga. Dukkan su kuma Fualani ne idan ka debe Matidan, wanda shi Balaraben Kano ne.

PTH: A sauran garuruwan ma haka ratar ta ke tsakanin Fulani da Hausawa?

KURAWA: Kwarai kuwa. Dalibin farko a Kwalejin Barewa ina jin a cikin 1923, mai suna Abubakar, Bafulatani ne daga Sokoto. Shi aka fara dauka a tarihin Kwalejin Barewa. Shi ne ma ya zama Madakin Sokoto daga baya. Dalibi na hudun dauka, Ahmadu Matidan ma dan Kano ne, amma Balarabe. Ahmadu Bello shi ne wanda ya fara zuwa Kwalejin Katsina daga cikin jinin Shehu Danfodiyo. Ina jin wajajen 1926. Da wannan ilmin ne Fulani su ka fara shiga gaban Hausawa wajen aikin gwamnati da kuma mulki na siyasa a tarihin Najeriya.

PTH: To tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Abdulsalami Abubakar fa? Wace kabila ce asalin sa?

KURAWA: Ba abin da na sani game da Abdulsalami. Abin da kawai na sani shi ne Bahaushe ne asalin sa. Ai ya na nan da ran sa, sai ka je ka tambaye shi. Ba zan iya kad-da-tarihin asali na mutum ba alhali ya na nan da ran sa (dariya).

PTH: Na san ba ka rasa abin cewa kan Ibrahim Babangida.

KURAWA: Duk wani abin da za a fada dangane da Babangida ya na cikin wannan littafin. (Ya nuna wa wakilinmu wani littafi na tarihin Babangida, bugun Turanci). Amma ka san mutane su na fadin abin da suka ga dama.

PTH: To kai kuma wane tarihi ka bari a Hukumar Bincike da Tattara Bayanai ta jihar Kano inda ka yi darakta? A lokacin gwamna Ibrahim Shekarau?

KURAWA: Na rike wurin tsawon shekara shida, daga 2005 zuwa 2011. Mun wallafa littatafai sama da 50, mun kuma rikodin na faya-fayai kamar 20.

PTH: A karshe, wane tasiri Fulani Gyanawa suke da shi yanzu a Kano?

KURAWA: Mu Gyanawa, kabilar Fulanin da Murtala Mohammed ya fito, a yau mu ne na biyu wajen yawan Hakimai A Kano. Ka ga dai ga Walin Kano, Matawalle, Dangoriba, Talba da Magajin Gari. Fulani Yolawa ne kadai su ka fi mu yawan Hakimai.

Dangoriba da na lissafa wanda ke kan sarautar Hakimin Tarauni, shi ne mahaifi na.

Share.

game da Author