Muhalli ke taimaka wa yara samun kashi 80% na kaifin fahimta – UNICEF

0

Asusun Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ta bayyana cewa yara kanana kan samu kashi 80% na kaifin fahimta ne daga yanayin wuraren zamantakewar da su ke.

Swadchet Sankey, wanda kwararren jami’in fannin ilimi ne na UNICEF, ta bayyana haka a wata hirar da da ta yi tare da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, a Abuja.

Ta yi kira ga mutane su daina alakanta kaifin kwakwalwar yaro da gado daga iyaye ko kuma salsalar da wasu ke cewa “ai abin a jini ya ke.”

Sankey ta jaddada cewa yanayin muhalin da yaro ya tashi a zamantakewar sa, ko kuma inda aka raine shi, shi ne ke shafar wakwalkwar sa, ko kwakwalkwar ta idan yarinyar mace ce, walau uba da uwar yaro dakikai ne ko masu ilmi.

Sai ta ci gaba da cewa yanayin inda yaro ya tashi kan iya yin tasiri ga daukacin rayuwar sa ko rayuwar ta.

“Duk da cewa salsalar halitta da yanayi su na da muhimmanci ga karuwar kaifin kwakwalwar yara, amma shi yanayin ya ma fi yin tasari matuka. Domin duk irin kaifin kwakwalwar iyaye, idan yanayin zamantakewar yaro ba kyau, to zai shafi kaifin kwakwalwar sa.

Daga nan sai Sankey ta fayyace lokutan da kwakwalwar yara ke fara tunbatsar kaifi, cewa daga farkon shekara zuwa shekara ta uku ta haihuwar yara.

A cewar ta, idan har za ka iya samun yaro wanda ya gaji kaifin kwakwalwa daga iyaye, amma kuma ba shi da abinci mai gina jiki, ga yawan laulayi sannan kuma ba shi da sukunin koyon ilmi a makatanta, kuma babu kyakkyawan rainon da ya samu, to hakan zai shafi kaifin kwakwalwar sa.

Ta ci gaba da cewa duk muhallin da ba shi da sukunin kare kananan yara daga kiyaye lafiyar su da samar musu abinci mai gina jiki, to ba cikakken muhalli ko yanayi ba ne da kan taimaka wa ci gaban kananan yara.

” Duk yaran da su ka tashi a cikin al’ummar da ke fama da kazamin rikice-rikice da gurbacewar muhalli da sauran su, to ba su zama hazikai, komin kaifin kwakwalwa da hazakar iyayen su.

A karshe ta yi kira ga iyayen yara ko masu kulawa da su, da su rika tantance tasirin yayanin da yaran su ke tashi a ciki domin kara musu kaifin fahimta, zurfin ilmi, zurfin tunani da kuma kaifin kwakwalwar da za su iya maida kasa zama kasaitacciya.

Share.

game da Author