‘Mugun halin su Odigie-Oyegun ne ya fitar da Atiku daga APC’, inji Timi Frank

0

Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Kasa, na jam’iyyar APC, ya bayyana cewa kalaman da Shaugaban Jama’iyyar APC na Kasa, John Oyegun ya yi wa Atiku bayan ya fice daga APC, kalamai ne irin na dan tasha.

Timi Frank, ya kara da cewa Oyegun ba shi da wata kimar da har zai soki lamirin Atiku Abubakar don ya yi fushi ya fice daga APC.

A cikin wata takardar da ya sa wa hannu kuma ya raba wa kafafen yada labarai, Timi Frank ya kara da cewa rashin iya shugabancin Oyegun ne ya haddasa har Atiku ya fice ya koma PDP.

Shi dai Oyegun ya bayyana cewa da fitar Atiku da tsayawar sa a APC, duk daya, ba shi da wani muhimmanci.

A kan haka ne Frank ya ce, “da Oyegun na da tunani da zaman jimami da zullumi ya kamata ya yi, ba ya soki Atiku ba.

Domin su Oyegun ne su ka taba harzuka Buhari har ya fice daga ANPP, amma a yau ta juyo shi ne shugaban kasa.”

“Idan sai bayan ka gama cinye albarkar mutum sannan daga baya ka dawo ka na aibata shi, to tun a duniya sai rayuwa ta yi maka alkalanci ta saka wa wanda ka aibata. Oyegun ne ya fi kowa cin moriyar Atiku a duk cikin ‘yan APC.” Inji Timi Frank.

Ya kara da cewa maimakon Oyegun ya yi karatun ta-natsu ya tashi ya dauki damarar gyaran matsalolin da ke cikin APC, sai ya ke bin ubangidan sa Atiku da bakaken kalamai.

A karshe ya yi nuni da cewa ya kamata Oyegun ya dauki darasi daga Bamanga Tukur, wanda suka fusata suka fice daga PDP domin sa. A karshe PDP ta yi asarar mulkin duk da karfin da ta ke da shi a wancan lokacin.

Share.

game da Author