MAULIDI: Maraba Da Shugaban Duka Annabawa

0

“Maraba da kai Muhammadu dan Amina,

Maraba da Shugaban duka Annabawa.

Muhammadu Sabulu mai wanke dauda,

Muhammadu magani mai warke kowa.

Ina dada godiya ga Ubangijinmu,

Da ya aiko ka domin kyautatawa.

Muhammadu yai kira mai so ya karba,

Wanda duk ke son ka ya wuce tabukewa.

Muhammadu son ka addini zakiyyi,

Tamat wa bi hamdihi mun ida waka,

Da ikon Rabbu Sarki mai iyawa.”

Share.

game da Author