Majalisar Tarayya ta hana Gwamnatin Buhari sayar da wasu kadarorin gwamnati

0

Majalisar Dattawa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da sayar da wasu kadarorin gwamnati da ta fara shirye-shiryen yi.

Kadarorin da ake kokarin sayarwa din sun hada Dandalin Wasan Gargajiya, National Theatre da kuma Dandalin Taro na Kasa, Tafawa Balewa Square. Dukkan su biyun a Lagos su ke.

Majalisar dai ta ce sayar da wadannan wuraren biyu mallakar gwamnati, tamkar ci wa Najeriya mutunci ne, ko kuma kwance mata zani a kasuwa.

Ana ganin cewa kasashen duniya su na da irin wadannan gine-gine, don haka bai kamata dukkan gwamnatocin da suka shude sun rike su, amma gwamnatin APC ta nuna kasa rike su, har ta nemi cefanar da su ba.

Tafawa Balewa Square dai a wurin ne aka fara yin bikin murnar samun ‘yancin Najeriya a 1 Ga Oktoba, 1960.

Da yawan mambobin majalisar dattawan sun yi tir da wannan aniya ta sayar da wuraren biyu. Wasu ma sun yi zafafan kalamai masu kaushi.

Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna, cewa ya yi, duk ma wani mai gurguwar tunani ko shawarar a sayar da wuraren, to shi ya je can wani wuri ya gina nasa idan har ya damu.

Share.

game da Author