Ma’aikatan jinya a Najeriya na da karancin horon ceto ran mara lafiya cikin gaggawa

0

Shugaban wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Inspire Nurses Network Africa INNA’ Josiah Okesola ya ce kashi 90 bisa 100 ma’aikatan jinya a kasar nan basu da horon kulawa da ceto rayukan mutane na gaggawa.

Ya ce kamata ya yi su sami horon da za su iya amfani da tausayi da hikima wajen kula da marasa lafiya a duk inda suka sami kansu musamman idan ana bukatan hakan cikin gaggawa.

Ya ce sanadiyyar hakan ya sa ake samun matsaloli wajen ceto rayukan mutane musamman wadanda ke fama da cutar bugawar zuciya da sauran su.

Share.

game da Author