Kwamishinan raya karkara na jihar Kano Kuma kanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Iliyasu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa shirin ziyarar Kano da Kwankwaso zai yi ranar Asabar mai zuwa ba zai yi wani tasiri ba GA masoya Buhari.
Ya ce Kwankwaso na so ya nuna wa mutane cewa zai iya hada kirjin sa da Buhari a jihar.
” Abin da na ke so Kwankwaso ya sani shine Buhari ba sa’an sa bane a Kano. Kanawa na Buhari ne ba na Kwankwaso ba. Duk abin da yake kokarin nunuwa ya sani tun yanzu na gaba yayi gaba.
Iliyasu yace Idan Kwankwaso bai manta ba, ya tuna yadda Buhari ya naka shi da Kasa a zaben fidda gwani a 2015. A haka ma Idan ya ce zai sake gwada takara da Buhari zai sha Kasa.
Ya Kara da cewa da gangar Kwankwaso yaki bin Buhari zuwa Kano saboda yana da wata boyayya duk da cewa duk sauran sanatocin da ke wakiltar jihar sun biyo Buhari.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba, Binta Sipikin ta maida wa Iliyasu martani cikin gaggawa inda ta ce Kwankwaso baya neman nuna isa ga kowa. Ta ce Kwankwaso zai zoyarci Kano ne domin ganawa da masoyan sa, sannan ya tattauna da sauran Yan siyasa da ke shirin tunkarar zaben kananan hukumomi a jihar.
Discussion about this post