Kungiyar asibitoci masu zaman kansu da hadin guiwar likitoci na GMD ta shigar da kara wata Kotu a Abuja tana neman ta tilasta wa karamar AMAC ta rage kudaden harajin da ta tsawwala wa asibitoci masu zaman kansu dake Abuja.
Shugaban kungiyar Chito Nwana yace suna rokon kotu ta bi musu didigin haka.
Ya ce suna biyan harajin rediyo da talabijin,harajin muhali,harajin kasuwanci da lasisin aiki da sauran su wanda idan aka ci gaba a haka zai durkusar da asibitocin.