Kungiyar Addinin Musulunci ‘MURIC’ ta yi Allah-wadai da Femi Fani-Kayode

0

Kungiyar Kare Lamurran Musulunci, MURIC, ta yi Allah-wadai da dan taratsi, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, dangane da kushe shigar hijabin da Amasa Firdaus ta yi, a lokacin bikin yaye daliban da suka karanci aikin shari’a.

MURIC ta ce kalaman Kayode rashin mutunci ne, rashin tashi a cikin kyakkyawar tarbiyya ne, sannan kuma tsananin tsana ne ya nuna ga addinin musulunci da musulmai.

Fani-Kayode dai ya soki lamirin shigar da Firdaus ta yi, ya na mai cewa bai kamata ba, kuma dakikanci ne, domin Najeriya dai kasa daya ce, amma ba mai bin addini daya na. Kuma taron da ta je ai ba taron addinin musulunci ba ne.

MURIC ta tunatar da Kayode cewa limaman kiristoci ma su na sa zumbulalliyar riga su je wuraren taron da ba na addinin musulunci ba. “Ko wani ya taba cewa tilas sai sun cire kayan su?” Inji MURIC.

“Ko zai yiwu nan gaba Fani-Kayode ya tsaya zabe har musulmi su zabe shi? Mu na jiran wannan rana ta zo. Yayin da ‘yan Najeriya nagari ke kokarin hada kan kasar nan? Femi ba ya komai sai rura wutar kabilanci, addinanci, kiyayya da fitintinu.”

MURIC ta ja kunnen sa da ya daina shiga sha’anin addinin Musulunci, ta kuma ja kunnen jama’a a yi kaffa-kaffa da shi.

Share.

game da Author