Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Ibe Kachikwu, ya gabatar wa Majalisar Zartaswa neman amincewar gudanar da kwangilar da a watannin baya ya zargi cewa Babban Daraktan NNPC, Maikanti Baru ya bayar ba da sanin sa ba.
Kachikwu ya shaida wa ’yan jarida a Fadar Gwamnati cewa an amince da aikin kwangilar gina bututun mai wadda a baya ya ce Baru ya bayar ga wani kamfanin kasar China.
Kwangilar dai ta kunshi har da aikin dasa bututun gas da za a yi na hadin-guiwa, da ya tashi daga Ajaokuta-Kaduna-Kano.
Idan ba a manta ba, wannan kwangila ce aka yi ta cece-ku-ce a kan ta watannin baya, inda Kachikwu ya yi zargin cewa Baru ya zagaye ya bayar da kwangilar ba tare da sanin sa ba.
Amma kuma sai ga shi a jiya Laraba, Kachikwu ya ce ya maido kwangilar ne domin ta samu amincewar Majalisar Zartaswa, kamar yadda tun da farko ya kamata a yi.
Discussion about this post