KUDIN MAKAMAI: Gwamna Fayose da Yari sun kwashi ‘yan kallo a Fadar Shugaban Kasa

0

Gwamnonin jihohin Ekiti da Zamfara, Ayodele Fayose da Abdul’aziz Yari, sun rika karyata junan su yau Talata a bainar jama’a, a dakin taro na Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.

Su biyun sun kaure ne yayin da Fayose ke ce wa Yari karya ya ke yi, gwamnoni ba su tattauna maganar amincewa a sayo makaman yaki da Boko Haram har na dala biliyan daya ba, shi kuma Yari na cewa karya Fayose ke yi, an tattauna, kuma gaba dayan gwamnonin suka yi jam’un amincewa da a fitar da kudin domin a sayo kayan yaki da Boko Haram.

Su biyun sun kaure da cacar-baki jim kadan bayan gwamnonin kasar nan sun yi taron ganawa da kakakin majalisun jihohin kasar nan baki daya, a Fadar Shugaban Kasa.

Gwamnan Etiki, Fayose, ya shaida wa manema labarai daga baya kafin ya bar fadar cewa tuni ya garzaya kotu, har ya shigar da kara cewa an yi masa kazafin amincewa da a cire kudin, alhalin bai ma san da batun ba.

Sannan kuma Fayose ya ce karar ta hada da kalubalantar cire makudan kudaden da za a yi, wadanda ya ce ya na son kotu ta haramta fitar da su.

Tun farko dai Fayose ne ya fara fitowa fili ya ce gwamnatin APC za ta fitar da kudin ne don kamfen na zaben 2019 kawai, amma ba don sayen makamai ba.

Share.

game da Author