Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP da su mai da hankali wajen ganin jam’iyyar ta sami nasara a zabukkan dake tafe.
Atiku ya bayyana haka ne da ya kai ziyara hedikwatar jam’iyyar a Abuja.
Bayan haka ya yi kira ga sauran mutane da suke son dawowa jam’iyyar da su gaggauta yin haka.
Shugaban jam’iyyar PDP Ahmed Makarfi ya yabawa Atiku sannan yayi masa alkawarin yin abin da ya dace ga duk dan jam’iyyar sabon shiga ko tsoho.
Discussion about this post