Kotu ta daure wani manomi da aka kama da aikata lalata da wata ‘yar shekara 14

0

Kotu a garin Ibadan jihar Oyo ta daure wani mutum mai suna Rafi’u Olagbenro a kurkuku da ta kama da laifin yin lalata da wata ‘yar shekara 14.

Dan sandan da ya shigar da kara Oluseye Oyebanji ya bayyana wa kotun cewa Rafi’u ya saba danne wannan yarinya a unguwan su dake kauyen Abendo duk lokacin da take hanyar dawowa daga makaranta.

Oyebanji ya ce matasan unguwan ne suka kama Rafi’u dumu dumu tare da wannan yarinyar a wata shingen gini bayan kakar yarinyar ta sa matasan unguwan neman ta domin yariyar bata dawo daga aiken da ta yi mata ba.

Bayan haka alkalin kotun Modupeola Olagbenro ta yanke hukuncin daure Rafi’u a kurkuku har sai ta gama sauraron shawarwari a hukumar da ake gurfanar da masu aikata laifuka na jihar sannan ta daga zaman kotun zuwa ranar 10 ga watan Janairun 2018 domin ci gaba da shari’ar.

Share.

game da Author