Kotu a Kaduna ta yanke hukuncin dakatar da gwamnatin jihar Nasir El-Rufai daga koran malaman makarantun firamaren jihar da suka fadi jarabawar gwaji, sama da 21,000.
Lauyan dake kare malaman da aka kora, Samuel Atum, ya shigar da kara kotu yana kalubalantar korar malaman da gwamnati tayi sannan da neman kotu ta dakatar da gwamnati daga yin hakan.
Alkalin Kotun Lawal Mani ya amince da wannan kara da hujjojin da Atum ya shigar gaban sa cewa, a dakatar da maganan sallamar malaman tukuna har sai kotu ta gama amsar bayanai akan dalilan yin haka. Bayan haka ya daga ci gaba da sauraron karar sai watan Fabrairun 2018.
Da muka nemi ji daga bakin Lauyan gwamnati, abin bai yiwu ba sai dai wata malama da ta zanta da wakilin mu a Kaduna ta ce abin da kotu tayi yayi daidai.
“ Wannan hukunci yayi daidai, yanzu dai muna zura ido mugani ko zai bi umarnin kotun.”
Discussion about this post