Ko gwamnati ta biya mu hakkokin mu, ko mu fara yajin aiki – Likitocin Jihar Kogi

0

Kungiyan likitocin Najeriya NMA reshen jihar Kogi sun kara yawan kwanakin da suka ba gwamnatin jihar ta biya
su hakkokin su ko su shiga yajin aiki.

Idan ba a manta ba kungiyar ta ce za ta fara yajin aiki ranar 24 ga watan Nuwamba idan gwamantin jihar bata biya musu bukatun su ba zuwa wannan lokaci.

Bayan haka ne shugaban kungiyar Godwin Tijani ya bayyana cewa bayyan tattaunawa da suka yi da gwamanti ranar 8 ga wannan wata, kungiyar ta amince ta fara yajin aiki idan har gwamnati bata cika alkawaruran da ta dauka na biya musu bukatun su ba nan da 31 da watan Disamba.

” Lalle za mu shiga yajin aiki ranar daya ga wantan Janairun 2018 idan har gwamnati bata biya mana bukatun mu ba.”

Bukatun sun hada da;

1. Rashin biyan likitoci albashi.

2. Likitocin su na so su biya haraji bisa karin girman da aka yi wa ko wani likita ko matsayin sa mai makon biya da suke yi bai daya.

3. Gwamnati ta biya albashin likitoci 8 da ta kora na watanni 12 da ta ke bin ta sannan ta biya albashin likitocin dake aiki a asibitocin jihar na tsawon watani 5.

4. Kungiyar ta ce gwamnatin ta biya albashin sabbin likitocin da ta dauka a watan Agusta 2017.

Share.

game da Author