Shugaban hukumar kula da amfani da magunguna da abinci ta Kasa, NAFDAC, Christiana Adeyeye ta yi kira ga mutane da su sa ido da tona asirin duk wadanda ke sarrafa jabun magunguna da suka sani.
Christiana ta ce haka zai taimaka wa hukumar wajen samun nasarar kawar da jabun magunguna daga kasar nan.
” Yin haka ya zama dole musamman gannin cewa masu sarrafa wadannan magungunan kan yi haka ne cikin dare a wuraren da suke hadawa.”
Daga karshe, ta bayyana cewa idan har jama’a suka hada hannu da ma’aikatan hukumar musamman wajen tona asirin masu sarrafa irin wadannan jabun magunguna za a sami raguwa wajen yawan yaduwar magungunar a kasa Najeriya.