KANJAMAU: Mutane 16,000 sun rasu a jihar Barno cikin shekara uku

0

Hukumar kula da masu fama da cutar kanjamau a Najeriya reshen jihar Borno NEPWAN ta ce a cikin shekaru 3 jihar ta rasa mutane sama da 16,000 sanadiyyar kamuwa da cutar kanjamau.

Shugaban hukumar Hassan Mustapha wanda ya bayyana haka ya ce dalilin samun karin yawàn mutanen dake dauke da cutar na da nasaba be da ayyukan Boko Haram a yankin wanda ke hana masu fama da cutar samun magani.

Ya kuma koka kan yadda yawan mutanen dake karbar magani ke raguwa a jihar.

‘‘A shekarar 2011 mutane 27,000 suka yi rajista don samun maganin cutar amma a 2017 yawan mutanen sun ragu zuwa 11,303.”

Share.

game da Author