Kamfanin Coca Cola ya gargadi mutane su rage shan Zaki

0

Kamfanin sarrafa Lemu na Coca Cola ya gargadi mutane da su rage shan zaki don lafiyar su.

Manajan kula da cinikayya na kamfanin Gbolahan Sanni, ne ya sanar da haka a wajen kaddamar da sabbin lemu da ga kamfanin.

Ya ce sabbin Lemun da suka fitar lemu ne da ya kunshi kayan itatuwa da jiki ke bukata.

Bayan haka ya yi kira ga mutane da su dinga amfani da irin wadannan lemu domin lafiyar jikin su sannan su rage shan zaki da yawa.

Share.

game da Author