Jami’ar IBB dake Lapai ta kara kudin Makaranta

0

Hukumar jami’ar Ibrahim Babangida dake Lapai jihar Neja ta kara kudin makaranta da zai fara aiki daga Shekara mai zuwa.

Shugaban jami’ar Mohammed Maiturare da ya sanar da haka ya ce karin ya zama dole saboda tsadar rayuwa da Kuma ganin yadda jami’ar ke kasa aiwatar da wasu muhimman ayyuka saboda rashin kudi.

‘‘Jami’ar ta yi tsawon shekaru 5 tana karban Naira 52,000 daga wajen daliban da ba ‘yan jihar ba saboda haka ba za su iya ci gaba da haka ba saboda karuwar bukatu da Jami’ar ke fama da su.

” Daga yanzu sabbin dauka Wanda ba ‘yan asalin jihar Neja bane za su biya naira 93,000 sannan ‘yan asalin jihar za su biya naira 52,000.”

‘‘Tsoffin dauka kuma da ba ‘yan asalalin jihar ba za su biya 55,000 sannan ‘yan jihar su biya 27,000’’.

Maiturare ya ce za su agaza wa daliban ta hanyar bada bashi da kuma damar biyan kudin makarantan kadan kadan wa duk dalibin dake bukata.

Share.

game da Author