INEC ta kori ma’aikatan da suka yi wa Gwamnan Kogi rajista kau biyu

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta kori wasu jami’an ta biyu saboda hannun da su ke da shi dumu-dumu a harkallar yi wa Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello rajistar zabe sau biyu.

Ana zargin gwamnan da yin rajistar jefa kuri’a sau biyu, a wurare daban-daban. Sai dai kuma shi har yau ya musanta wannan zargi da ake yi masa.

A wata takarda da Hukumar Zabe, INEC ta fitar yau Alhamis, ta bayyana cewa, “hukumar ta nada kwamitin bincike, sakamakon wani ratoho da ta samu cewa an yi wa Gwamnan Kogi rajista har sau biyu.”

Hukumar ta ci gaba da cewa ba za ta iya gurfanar da Yahaya Bello ba a yanzu, saboda ya na da dokar kariya a kan sa, a matsayin sa na gwamna.

Duk da cewa shi gwamnan na Kogi ya na da dokar kariya a wuyan sa, hukumar zaben ta zartar da wadannan hukunce-hukunce.

* Korar ma’aikatan INEC biyu da ke da hannu cikin harkallar.

* Gaggauta yin ritaya ga wani Babban Jami’in Zabe daya saboda shi ma an kama shi dalaifi’

Share.

game da Author