INEC ta daga darajar ma’aikata 4,917

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana karin mataki da daga darajar ma’aikatan ta har su 4,017.

An kara musu matakan ne bayan sun zauna jarabawar gwajin cancanta a cikin watan Satumba da kuma Nuwamba, 2017.

An gudanar da jarabawar ne a hedikwatar hukumar da ke Abuja da kuma sauran jihohin kasar nan.

INEC ta yi bayanin sakamakon jarabawar, dalla-dalla , inda ta ce kashi 92.1℅ na manyan ma’aikatan hukumar da ke kan matakin albashi na 07 zuwa 15 su ka samu nasarar jarawabar.

Wato kenan manyan ma’aikata 4,917 daga cikin 5,335 da ke a karkashin hukumar.

Sai kuma ma’aikata 326 wadanda ba su yi nasarar jarabawar ba, ko kuma suka ki zama su rubuta jarabawar.

INEC ta kuma amince da adadin kananan ma’aikatan ta su 2,413, wadanda ke matakin albashi na 03 zuwa 06. Ta na mai cewa an gudanar da kwarya-kwaryar jarabawar ne domin a kara wa ma’aikata kwarin guiwa ta hanyar kara kulawa da su yadda za su kara himma wajen kishi da gudanar da ayyukan su.

Alhaji Baba Shettima Arfo shi ne Shugaban Kwamitin Nada Mukamai, Karin Girma da kuma Ladabtarwa.

Share.

game da Author