Ina kalubalantar Atiku ya kawo shaidun cewa ya taimaka wa Kamfen din Buhari a 2015 – El-Rufai

0

Gwamnna jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya karyata dalilan da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya fadi wai sune suka ingiza shi ficewa daga jam’iyyar APC.

A hira da El-Rufai yayi da gidan radiyon muryan Amurka, VON, ya ce ba gaskiya ba ne dalilan da Atiku ya bada wai sune silar ficewar sa daga jam’iyyar APC kamar wai an yi watsi da shi bayan gudunmuwar da ya bada jam’iyyar ta samu nasara a zabukan 2015.

El-Rufai ya ce idan Atiku na da shaidar cewa ya ba Buhari gudunmuwa a zaben 2015 ya kawo su ko kuma ya baza kowa ya gani. Ficewar sa bata da nasaba da abin da yake ta yayadawa, kawai don cika wata buri ce tasa, shine dalilan da ya sa ya tattara nasa-ina-sa ya koma PDP.

” Lallai dole ne idan mutum ya fadi zabe zai dan ji ba dadi amma maganganun da Atiku ya ke ta yi cewa wai APC sun yi amfani da kudin sa a 2015 ba haka bane. Ya fito ya gaya mana wa yaba kudin da yake cewa ya bada, ni dai na san duk wadan da suka taimaka mana da kudaden su da kaddarorin su da mukayi amfani dasu a lokacin zabe. Kuma ban taba jin wai Atiku ya ba da ko sisi ba. Idan kuma haka ne, toh wa yaba? Ya fito ya fadi wa jama’a sannan ya fadi abin da aka yi da su.”

El-Rufai ya ce tun bayan amincewa da gwamnonin kasar nan su kayi da tsayar da Buhari, hankalin Atiku ya tashi, ya kasa samun natsuwa har sai da ya koma PDP.

Ko da yake hirar VOA ba da shi kadai bane a kayi, shi kan sa Atiku da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido sun tsokata a hirar.

Da yake amsa wasu tambayoyin da aka yi masa Atiku Abubakar ya ce har yanzu bai gama shawara ba game da inda ya dosa a siyasan ce tun bayan komawar sa PDP.

Shi ko Sule Lamido a na shi bayanan, cewa yayi duk da murna da suke yi na dawowar Atiku jam’iyyar PDP, hakan ba shine zai sa wai ya hakura da burin sa na neman yin takarar shugaban cin kasar nan ba.

Share.

game da Author