Yan uwan marigayiya Sandra David sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa har yanzu babu wani abu da akayi game da kashe ‘yar uwar su da wasu dakikan likitoci suka yi a asibitin gwamnati dake Abuja.
Duk da cewa tun bayan rasa ranta da tayi mahaifiyar Sandra ta garzaya Kotu domin abi mata hakkin ta kan abin da akayi wa ‘yar ta. Sannan kuma kungiyoyin likitoci na kasar nan duk suna da masaniya kan abin da ya gfaru da marigayiya Sandara abin dai shiru kamar an ci shirya.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta rawaito a watan Disambar 2016 yadda sakacin likitocin asibitin gwamnati dake Abuja suka yi sanadiyyar rasuwar Sandra da wasu jarirai uku a asibitin.
Bisa ga bayanan da Sophia David kanwar mamaciyar ta bayar ta ce daga neman maganin yoyon fitsari wanda shine sanadiyyar kai Sandra asibiti, kafin su ankara likitocin sun fara yi musu bayannan boge wanda daga baya suka dinga jujjuya su suna danganta ciwon Sandra da wasu cututtuka da ba haka.
Likitocin sun ce wai ta kamu da cutar Koda, sannan tana dauke da Kaba a cikin ta wanda daga baya aka gano duk ba haka bane bayan sun kai ta wani asibiti mallakar kasar Turkiyya inda anan ne suka tabbatar musu cewa wadannan likitoci na farko sun la’anta Sandra, kuma ba su da yadda za su yi da ita. Ana haka ne wa’adi ya iske Sandra tace ga duniyar nan.
Kungiyar Likitoci na kasa da kotu da aka shigar da kara akan abin da akayi wa Sandara sun kasa yin wani abu akai shekara daya kenan bayan rasuwar ta.
Tajudden Sunusi, shugaban kungiyar likitoci MDCN, yace kungiyar sa na yin wani abu aki sai dai ba zai iya fadin komai ba sai sun kammala domin abin suna yin sa ne cikin sirri.
Ita ko karar da aka shigar kotu, ba a ce komai ba har yanzu akai. Kullun idan zaman ci gaba da sauraron karan yayi sai a daga.