Hana cin hanci da rashawa ya fi sauki bisa ga yaki da masu ci – Magu

0

Shugaban Rikon Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa hana cin hanci da rashawa ya fi sauki fiye da yaki da masu cin hanci da rashawa.

Magu ya yi wannan bayani a jiya Alhamis ya wani taron wayar da kai kan hana cin hanci da rashawa wanda Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Sama, FAAN ta shirya a Abuja.

Ya ce sashe na 6 na dokar EFCC ta bayyana cewa hanyoyin hana cin rashawa sun hada har da kamfen tukuru ana wayar wa jama’a kai dangane da mummunar illar cin hanci da rashawa.

“Saboda EFCC ita kadai ba ta iya kawar cin hanci ita kadai. Zan yi amfani da wannan dama na bayyana muku cewa cin rashawa ya yi wa gaba dayan mu illa a kasar nan.

“Tilas sai mun tashi haikan mun yi yakin kakkabe rashawa da cin hanci a kan tafarkin da Shugaba Muhammadu Buhari ke yawn jan hankalin mu mu rika yi.

Share.

game da Author