Gwamnatin Zamfara ta fara biyan wadanda aikin hanya ya shafi gidajen su

0

A yau ne gwamnatin jihar Zamfara ta ware Naira miliyan 100 don biyan wadanda gwamnati za ta yi amfani da filayen su a Talatan– Mafara domin fadada hanyoyi a yankin.

Kwamishinan filaye Ahmed Sharu ya sanar da haka a wajen mika wa mutanen da ya shafa kudaden a fadar sarkin Talatan-Mafara ranar Laraba.

Ya ce bayan sun kammala biyan su kudaden gwamnati za ta fara rusa gidaje da shagunan mutanen da ke wuraren da za a fadada hanyoyin.

Daga karshe ya yi kira ga masu gine-gine da masu filaye a wurin da su bada hadin kai.

Share.

game da Author