Gwamnatin ta ware biliyoyin naira don gyara cibiyoyin kiwon lafiya a kasar nan

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce gwamantin tarayya ta tanadi Naira biliyan 28 domin gyara cibiyan kiwon lafiya a matakin farko dake kananan hukumomin kasar nan a 2018.

Za a gyara cibiya daya a kowani karamar hukuma sannan gwamnati za ta gyara manyan asibitoci.

Ya ce hakan zai yiwu ne ganin cewa tun a baya gwamnati tayi alkawarin gyara cibiyoyin kiwon lafiya 10,000 a kasar nan.

Duk da hakan Adewole ya ce gwamnati ta dauki ma’aikata 200,000 domin bunkasa yin alluran rigakafi, awon ciki da sauran kulan da mutanen karkara ke samu a asibitocin yankunan su.

Ya kara da cewa za su yi amfani da wannan kudaden wajen karo maganin cutar kanjamau akalla na mutane 20,000 tare da yi wa mata gwajin cutar dajin dake kama al’aura, marainan maza da dajin dake kama nono.

Ya ce za kuma a yi fidar cutar amosanin ido wa mutane 250 a duk jihohin dake kasar sannan da kula da mutanen dake dauke da cutar ‘Hepatitis C’ duk kyauta.

Daga karshe Adewole ya ce Hukumar inshoran lafiya ta kasa za ta tallafa wa manyan asibitocin kasar nan da kudade don inganta kulan da ake ba mutane a asibitocin.

Sai dai kuma watanni 10 da daukar wannan alkawari na gyara cibiyoyin kiwon lafiya da gwamnati tayi, a wani bincike da PREMIUM TIMES ta yi ta gano cewa wasu asibitocin dake jihohin Neja, Benue da Nasarawa na fama da karancin magunguna, kayan aiki, ma’aikata da sauran su.

Share.

game da Author